Najeriya

Baraka na fitowa fili tsakanin Saraki da fadar Buhari

Shugaban Majalisar Dattijai Dr Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu na ratsuwar kama aiki
Shugaban Majalisar Dattijai Dr Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu na ratsuwar kama aiki hopefornigeriaonline

Bisa dukkan alamu baraka tsakanin bangaren shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da bangaren shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki na dada fitowa fili, ganin irin kalaman da kowanne bangare ke firtawa. 

Talla

Bayan gurfanar da Saraki da wasu jami'an majalisar dattawa a gaban Kotu saboda zargin su da sauya dokar majalisar, Sanata Saraki ya zargi wasu mutane da karbe ragamar tafiyar da kasar don neman biyan bukatun kansu.

Saraki ya kara da cewar a shirye yake ya je gidan yari don kare martabar Majalisar kasar.

Sai dai wadannan kalamai ba su yi wa bangaren shugaban kasar dadi ba, inda mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya musanta ikrarin kana ya  bukaci Saraki ya bayyana sunayen wadanda suka karbe ragamar, inda yake cewar shugaba Buhari ba karen farautar wani ko wasu mutane bane.

A jiya ne mai shari'a na babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja, Yusuf Haliru ya bada belin Saraki da mataimakinsa, Ike Ekweremadu da tsohon akawun majalisar tarayya, Salisu Mai kasuwa da mataimakinsa Ben Efeturi, inda ya gindaya musu wasu sharudda na samun belin, ciki kuwa har da gabatar da mutumin da ke da gida a Abuja.

Lauyan saraki, Joseph Daudu ya yiwa  wakilinmu na Abuja Aminu Manu karin bayani kan belin.

Joseph Daudu kan belin Saraki da mukarrabansa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.