Najeriya

Mark ya hana sanatocin Najeriya tsige Buhari

Mambobin majalisar dattawan Najeriya
Mambobin majalisar dattawan Najeriya

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya sanata David Mark ya hana majalisar   daukan matakin tsige shugaba Muhammadu Buhari daga karagar mulki.

Talla

Wasu daga cikin mambobin majalisar da ke mara wa Bukola Saraki baya sun yi yunkurin tsige Buhari a zaman sirrin da suka yi jiya Talata, yayin da David Mark ya bukace su da su janye matakin don kubutar da martabar majalisar a idon ‘yan Najeriya.

Daukan matakin dai nada nasaba da tuhumar da ake yi wa shugaban majalisar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu kan zargin sauya dokokin majalisar.

Rahotanni sun ce, Sanata Enyinnaya Abaribe na jam’iyyar PDP daga jihar Abia ne, ya fara kawo shawarar tsige Buhari bayan kwamintin majalisar da ke kula da harkokin shari’a da kare hakkin dan Adam ya sanar da kalubalen da ya ke fuskanta wajen gurfanar da babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami a gaban majalisar.

Shugaban kwamitin David Umaru ya ce, Malami ya ki mutunta gayyatar da aka yi masa don amsa tambayoyi kan tuhumar Saraki da mataimakinsa da wasu ‘yan majalisun biyu.

Rahotanni sun ce Mr. Mark ya taka rawa wajen hana sauran sanatocin PDP daukan matakin tsige shugaba Muhammadu Buhari da suke ganin yana da hannu wajen hana babban sufeto janar na ‘yan sandan kasar kama Abubakar Malami saboda kin mutunta gayyatar da aka yi masa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.