Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta haramta karin kudin wutar lantarki a Najeriya

'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan rashin wadatacciyar wutar lantarki gami da matsalar karancin man fetir
'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan rashin wadatacciyar wutar lantarki gami da matsalar karancin man fetir AFP Photo / Leo RAMIREZ
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Babbar kotun tarayya da ke birnin Legas na Najeriya ta haramta karin kudin wutar lantarki da gwamnatin kasar ta yi na kashi 45 cikin 100, inda ta bukaci janye karin nan take da kuma jan kunnen hukumar samar da wutar wajen yin wani karin ba tare da la’akari da dokar sauyin da aka yi wa harkar samar da wutar ba.

Talla

Alkalin kotun Ibrahim Idris ya bayyana karin wanda aka yi shi cikin gaggawa a matsayin babban kuskure wanda ya saba wa dokar kasa.

Wannan hukucin ya yi wa kungiyar kwadago ta kasar dadi ganin yadda ta jajirce don ganin karin bai samu nasara.

A bangare guda, a farkon makon nan ne, kamfanonin da ke samar da wutar lantarki a Najeriya suka sanar da shirinsu na sake kara kashi 100 na kudaden wutar da talakawa ke sha, lamarin da ya gamu da suka daga ‘yan kasar da kungiyar masu masana’antu wadda ta kalubalaci matakin a hukumar kula da wutar lantarki ta kasar.

Majalisar wakilai ta nuna rashin gamsuwarta da matakin baya-bayan nan, inda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta dakatar da karin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.