Najeriya

Avengers sun yi alkawarin dakatar da hari a Najeriya

Tsagerun Niger Delta Avengers sun yi alkawarin dai kai hare hare kan bututun mai a Najeriya
Tsagerun Niger Delta Avengers sun yi alkawarin dai kai hare hare kan bututun mai a Najeriya AFP/PIUS UTOMI EKPEI

Tsegrun kungiyar Niger Delta da ke kudancin Najeriya sun yi alkawalin dakatar da kai hare-hare kan bututun mai da kadarorin gwamnati da ke yankinsu.

Talla

Kusoshin kungiyar suka tabbatar da haka a tattaunawar da su ka yi da Ministan wasanni da matasa na kasar, Barista Solomon Dalung a yankinsu mai arzikin man fetir.

A hirarsa da sashen hausa na rfi, Dalung ya ce, sai da suka shafe tsawon sa’oi biyu cikin kwale- kwale a kan ruwa tare da mambobin kungiyar kafin su kai inda su ka yi zaman tattaunawar.

Ga abinda ministan ya shaida wa Awwal Janyau

Solomon Dalung kan ganawarsa da Avengers

Hare haren da kungiyar ke kai wa kan kadarorin gwamnati da bututun main na kamfanoni da bana dabamn sun haifar da nakasu ga tattalin arzikin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.