Najeriya

Damar sanya hijabi a makarantun gwamnati dake jahar Lagos

Yan makaranta sanye da hijabi
Yan makaranta sanye da hijabi www.pmnewsnigeria.com

Kotun daukaka kara a Lagos ta baiwa yaran Musulmi damar sanya hijabi a makarantun gwamnati daga Firamare zuwa Sakandare, sabanin dokar da gwamnatin Jihar tayi a baya.

Talla

Alkalin kotun da ya jagoranci takwarorin sa wajen bayyana hukuncin AB Gumel yayi watsi da umurnin babbar kotun Jihar na haramtawa daliban sanya hijabin.

Hukuncin ya haifar da murna ga daruruwan mutanen da suka halarci zaman kotun, wadanda suka dinga kabbara.

A baya can an hana yara musulmi sanya hijabi zuwa makarantun gwamnati bisa umarnin babbar kotun jihar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.