Najeriya

'Yan sanda sun hana PDP taro a Fatakwal

'Yan sanda sun rufe fillin taron PDP a Port Harcourt
'Yan sanda sun rufe fillin taron PDP a Port Harcourt

Rahotanni daga birnin Fatakwal sun ce, ‘yan sanda sun killace fillin kwalon Sharks da Jam’iyyar PDP ke shirin gudanar da taron ta na kasa yau laraba.

Talla

Kakkakin ‘yan sanda a jihar Rivers, Nnamdi Omoni dake tabbatar da haka ya ce sun Killace fillin ne bisa umarni kotu.

Da aka tambaye Omoni, batun hukuncin kotu mai karo da juna kan taron, sai ya nuna ba shi da masaniya.

Kamfanin dilancin labaran Najeriya ya rawaito cewa jami’an tsaro sun hana mahalarta taron da 'yan jaridu shiga fillin da aka shirya taron.

A jiya babbar kotun Abuja ta haramta gudanar da taron tare da umarta ‘yan sanda da Jami’an hukumar zabe ta kasa wato INEC kauracewa gangamin.

Hakan na zuwa ne bayan wata babbar kotun da ke zamanta a Fatakwal ta bayar da umarnin a yi taron.

Yunkurin daidaita bagarorin da ba sa ga maciji da juna a Jam'iyyar na Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi ya ci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.