Najeria

Ezekwesili ta bukaci gaggauta hukunci kan masu laifi a Najeriya

Daya daga cikin Iyayen 'yan matan Chibok da aka sace
Daya daga cikin Iyayen 'yan matan Chibok da aka sace REUTERS

Kungiyar Bring Back Our Girls (BBOG) mai neman a ceto ‘yan mata na makarantar Chibok daga mayakan Boko Haram, ta bukaci hukumomin Najeriya sun gaggauta hukunta wadanda suke da hannu a badakalar sayan makamai lokacin gwamnatin da ta shude. 

Talla

Shugabar kungiyar ta BBOG, Oby Ezekwesili, ta bukaci hakan a taron suka gudanar ranar Talata, ranar da kwanaki 869 suka cika da sace ‘yan makarantar Chibok sama da 200 da mayakan Boko Haram suka yi a shekara ta 2014.

Ezekwesili ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci ofishin Ministan Shari’ah na Najeriyar, da Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, su kafa kotun musamman da zata saurari tuhumar masu laifin, tare da yanke musu hukunci cikin gaggawa.

Mai Magana da yawun kungiyar, ta kuma bukaci a daina yawaita dage sauraron shari’ar da ake yiwa masu hannu kan badakalar sayan makamai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.