Najeriya

Hukumomi suna kokarin farfado da tattalin arzikin Najeriya

Bayan Kwashe watanni 6 Najeriya na fama da fashe fashen bututun mai da ya kassara kudaden shigar ta, da kuma faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, ana saran gwamnatin kasar sanar da shiga matsalar tattalin arziki a hukumance.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP via telegraph
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar raguwar kudaden shiga da faduwar darajar kudin kasar ya tilastawa gwamnati tsuke bakin aljihun ta da hana shigar da kayan abinci da ake iya noma su a cikin gida, abinda ya haifar da tsadar abincin da kuma korafi daga jama’ar kasa.

Yayinda ita kuma gwamnatin Najeriya ke nanata cewa matsin dan lokacine nan gaba kadan mutanen kasar zasu dara.

Sai dai rahotanni sun ce yanzu haka wasu yan kasuwa na almundahana wajen hada shinkafar gida da ta waje inda suke sayar da ita a farashi mai tsada.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI