Najeriya

Rikici ya barke tsakanin 'ya'yan Boko Haram

An kashe bangaren Abubakar Shekau a fafatawar da ya yi da bangaren Al-Barnawi
An kashe bangaren Abubakar Shekau a fafatawar da ya yi da bangaren Al-Barnawi HO / BOKO HARAM AFP / AFP

Rahotanni daga Najeriya na cewa, rikici ya barke tsakanin mambobin kungiyar Boko Haram da suka rabu gida, inda suka kashe junansu.

Talla

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, bangaren Abu Musab al-Barnawi, ya hallaka mayaka da dama daga bangaren Shekau a dauki-ba-dadin da suka yi a Mongunu da ke jihar Borno.

Tun bayan da kungiyar IS ta sanar da nadin Barnawi a matsayin sabon jagoran kungiyar, mambobinta suka kasu gida biyu.

Sai dai duk da wannan sanarwar, Abubakar Shekau ya jajirce cewa, shi ne shugaban kungiyar wadda ta kashe dubban mutane tun daga shekarar 2009 tare da tilsta wa miliyoyi kaurace wa giudajensu.

Rikicin kungiyar na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojin Najeriya ke ci gaba da kokarin kakkabe ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.