Isa ga babban shafi
Njeriya

Amurka ta taya Najeriya murnar cika shekaru 56 da samun 'yancin kai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Gwamnatin Amurka ta taya Najeriya murnar cika shekaru 56 da samun ‘yancin kai, a yau 1 ga watan Oktoba shekara ta 2016.

Talla

Cikin sakon taya murnar daga Shugaban Amurka Barrack Obama, wanda sakataren harkokin wajen kasar John Kerry ya fitar, ya ja hankalin shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, kan har yanzu gwamnatinsa na da sauran aiki da suka kunshi karasa murkushe mayakan Boko Haram, da kuma kakkabe cin hanci da rashawa domin cimma burin ciyar da kasar gaba.

Sai dai Kerry ya bayyana gamsuwa da kokarin da gwamnatin Najeriyar ke yi na shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta musamman na tattalin arziki da tsaro.

Obama ya kuma jaddada aniyar Amurka na karfafa dagantaka tsakaninta da Najeriya domin ciyar da ita gaba dama nahiyar Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.