Isa ga babban shafi
Najeriya

Cin hanci ya ci kujerar alkalai 3 a Najeriya

Matsalar cin hanci da rashawa na ciwa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya.
Matsalar cin hanci da rashawa na ciwa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya. © RFI
Zubin rubutu: Ramatu Garba Baba
Minti 2

Hukumar da ke sa ido kan harkokin shari’a ta sanar da korar wasu manyan alkalai 3 daga bakin aiki bayan samunsu da laifin cin hanci.

Talla

Kakakin hukumar Mr Soji Oye yace hukumar ta bukaci alkalan da su yi murabus dole bayan an samesu da aikata laifukkan da ke da alaka da karbar rashawa.

Alkalan uku sun hada da mai shari’a Kabiru Auta alkalin kotun jahar Kano da alkalin kotun daukaka kara dake a Illori a jahar Kwara mai shari’a Mohammed Ladan Tsamiya sai kuma babban alkalin kotun Enugu mai shari’a Mr I A Umezulike.

An dai sami Mr Umezulike da hannu dumu dumu a badakalar cin hanci da ya shafi zaben 2015 hakazalika mai shari’a Ladan Mohammed.

Daman Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sha zargin alkalan da laifin yin ba daidai ba a hukuncin da suke yankewa wasu da ake zargi da rashawa, a yayin da gwamnati ke kokarin kubutar da kasar daga matsalar rashawa da ya yi mata katutu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.