An gudanar taron inganta kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar a Jihar Jigawa

Gwamnan Jigawa Alhaji Badaru Abubakar
Gwamnan Jigawa Alhaji Badaru Abubakar jigawastate.gov.ng

An gudanar da wani taro a jihar jigawa da ke arewacin Najeriya da nufin inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da janhuriyar Nijar. Jihohin jigawa Kano da Katsina da suka yi iyaka da janhuriyar ta Nijar ne ke ganawa da Wata tawaga karkashin jagorancin gwamnan Damagaran Malam Issa Musa, a wani mataki na bijiro da hanyoyin kaucewa dogaro da man fetur don inganta fatauci tsakanin kasashen biyu.  

Talla

CORRESP-DANDAGO-2016-09-29

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI