Najeriya

Mun kori Rahma Sadau daga masana'antar shirya Fim-MOPPAN

Fitacciyar jarumar fina-finan hausa, Rahma Sadau
Fitacciyar jarumar fina-finan hausa, Rahma Sadau Kannywoodtoday.com

Kungiyar kula da harkokin shirya fim din Hausa MOPPAN ta bayyana bacin ranta game da wani bidiyon waka da ‘yar fim din Hausa Rahama Sadau ta bayyana a ciki tana rungumar wani mawaki ‘Classiq’.

Talla

Kabiru Maikaba wanda shi ne shugaban kungiyar ya ce bidiyon wakar ba shakka zubar da kima ce ga masana'antarsu kuma zai lalata kyakkyawar dangantakar da take tsakaninsu da jama’a.

Cikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar ta MOPPAN salisu Muhammed ya fitar ya ce domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro yasa bayan gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan harkar shirya fim na Hausa, kungiyar ta MOPPAN ta amince da korar Rahama Sadau daga masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Kungiyar tace wannan shine karo na uku da ake ladabtar da ita kan laifufukan da take yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.