Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta kwace kadarar Orubebe

Godsday Orubebe, Tsohon Ministan Niger Delta a lokacin da yake kalubantar tattara sakamakon zaben 2015 a gaban Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC
Godsday Orubebe, Tsohon Ministan Niger Delta a lokacin da yake kalubantar tattara sakamakon zaben 2015 a gaban Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Kotun ladabtar da ma’aikata ta Najeriya ta kwace kadarar tsohon ministan Niger Delta Godsday Orubebe sakamkon bayar da bayanan karya dangane da dukiyar da ya mallaka a lokacin da yake rika da mukamin ministan.

Talla

Kotun karkashin shugabancin Danladi Umar ta kwace kadarar ce wadda Mr. Orubebe ya ki shigar da ita a cikin takardun bayanan kadarorinsa, amma ba ta ci wata tara ba.

An dai bayyana kadarar a matsayin wani fulotin kasa da ke Asokoro na birnin Abuja yayin da rahotanni ke cewa, Orubebe ya mallaki fulotin ne gabanin saukarsa daga kujerar minista da wata guda.

Tsohon Ministan ya ce, ya sanya fulotin mai lamba 2057 a kasuwa gabanin wa’adinsa ya kawo karshe.

Mr. Orubebe dai ya shahara wajen nuna goyon bayan ga tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, kuma shi ne ya kusan tayar da hatsaniya a lokacin da ake tattara sakamakon zaben 2015 wanda ya bai wa shugaba Muhammadu Buhari nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.