Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya zata dauki sabbin malaman makaranta 200,000

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kammala tantance wadanda zata dauka a matsayin sabbin malaman makarantu a kasar.  

Talla

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce a karshen watan Oktoba ake sa ran fara aikin sabbin malaman 200,000, kashi na farko kenan daga cikin 500,000 da gwamnati ta yi alkawarin dauka.

Tun bayan cire tallafin man fetur da take samarwa, gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin daukar dalibai 500,000 da suka kammala makarantun gaba da sakandare da basu da sana’a ko aikin yi.

Mataimakin shugaban Najeriya Osinbajo, ya kuma kara da cewa a watan Oktoban da ake ciki, gwamnatin kasar zata cika alkawarin bawa masu sana’ar hannu, mata, da sauran ‘yan kasuwa da suka cancanta miliyan daya, bashi mai rahusa da zai kama daga Naira 60,000 zuwa 100,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.