Isa ga babban shafi
Najeriya

An saki 'yan Matan Chibok 21

'Yan matan Chibok a wani fai-fai bidiyo da Boko Haram ta fitar a baya
'Yan matan Chibok a wani fai-fai bidiyo da Boko Haram ta fitar a baya AFP
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Gwamnatin Najeriya ta sanar da sakin 'Yan matan makarantar Chibok 21 daga cikin sama da 200 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su sama da shekaru biyu.

Talla

Mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya ce yanzu haka 'Yan matan 21 na hannun hukumar jami'an tsaron farin Kaya ta DSS.

Garba Shehu ya ce shugaban hukumar Lawal Daura ya yi wa shugaban kasa bayani kan sakin 'Yan matan biyo bayan bayan tattaunawar da ake tsakanin shugabannin kungiyar Boko haram da gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin kungiyar agaji ta Red Cross da gwamnatin Switzerland da ke shiga tsakani.

Ana sa ran Mista Daura ya mikawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo 'Yan matan nan gaba saboda shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Jamus domin tattaunawa da Angela Merkel game da batutuwan da suka shafi yaki da ta'addanci da kwararar 'yan ci rani zuwa Turai.

Majiyoyi sun ce an saki 'Yan matan ne a musayar da ta shiga tsakanin Fursunonin Mayakan 4 da ke gidan yarin Banki a  arewacin Najeriya da kuma 'Yan makarantar 21.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.