Isa ga babban shafi
Najeriya

NJC ta haramta wa alkalan Najeriya karbar kyauta

Shugaban alkalan Najeriya, mai shari'a  Mahmud Mohammed
Shugaban alkalan Najeriya, mai shari'a Mahmud Mohammed vanguardngr.com
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Hukumar kula da ayyukan shari’a ta Najeriya ta haramta wa alkalai da ma’aikatan kotuna karbar duk wata kyauta daga bangarorin gwanmnati.

Talla

Har ila yau, hukumar ta haramta wa alkalanta da hukumomin da ke karkashinta neman wata alfarma daga bangarorin gwamnatin, a wani mataki na inganta ayyukan shari’a a kasar.

Matakin dai zai dakile matsalar cin hanci da rashawa da miyagun dabi’u da suka ci karo da dokoki da wasu alkalai da ma’aikatan kotuna ke nunawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi dirar mikiya a gidajen wasu manyan alkalan kasar da suka hada da na kotun koli da na babbar kotu a wasu jihohin kasar.

DSS ta ce, jami’anta sun samu miliyoyin kudi a gidajen alkalan da ake zargi sun karbi cin hanci.

To sai dai a bangare guda, hukumar ta NJC ta ce, ba za ta dakatar da alkalan da suke fuskantar shari’a daga gudanar da ayyukan su ba.

Wannan ya biyo bayan shawarar da kungiyar lauyoyi ta bayar cewa, bai dace alkalan da ke fuskantar shari’a a wata kotu ya kasance kuma suna gudanar da shari’a ba, saboda haka ya dace a dakatar da su har sai sun wanke kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.