Najeriya

Walter Onnoghen ne sabon Alkalin alkalan Najeriya

Wata babbar kotun tarraya a Abuja.
Wata babbar kotun tarraya a Abuja. http://nigerianpilot.com

A yau Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Walter Onnoghen daga Jihar Akwa Ibom a matsayin sabon babban mai shari’a na kasar na riko, sakamakon kawo karshen aikin Mahmud Muhammad a daren laraba.

Talla

Sama da wata guda Hukumar dake kula da ayyukan shari’a ta mika wa shugaba Buhari sunan Mai Sharia Onnoghen dan gabatar wa Majalisar Dattawa domin amincewa da nadin nasa, amma kuma rahotanni na nuna cewar shugaban bai gabatar da sunan ba.

Ma’aikatar Shari’a a Najeriya ta fuskanci zarge-zarge da suka kunshi batutuwan cin hanci da rashawa daga manyan alkalan kotun.

A baya jami’an tsaro sun yiwa alkalai dirar mikiya inda suka kama bakwai daga cikinsu an kuma gano makuddan kudade na waje a gidajen alkalan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.