Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi barazanar daukar mataki kan Ministan Shari'ah

Ministan Shari'a na Najeriya Justice Abubakar Malami
Ministan Shari'a na Najeriya Justice Abubakar Malami

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi barazanar bada izinin kama Ministan Shari’ah na kasar, Justice Abubakar Malami.

Talla

Majalisar ta ce dalilinta shi ne rashin mutunta bukatarta da Ministan yayi, na bayyana gaban kwamitin da ke bincike kan sumamen da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kai kan gidajen wasu alkalai da ake zargi da almundahana.

Kamar yadda kafafen yada a Najeriya suka rawaito, shugaban kwamitin da Majalisar Wakilan ta kafa, don bincika batun kai sumamen, Garba Datti, ya ce sau biyu suna aikewa da wasika ga Ministan Shari’ar, domin bayyana gaban kwamitin, amma bai bada amsa ba, ballantana ya amsa bukatar.

Ranar Alhamis din da ta gabata, Majalisar Wakilan Najeriyar ta bukaci,Ministan Shari’a Justice Abubakar Malami, Daraktan hukumar tsaro ta DSS, Lawal Daura, da kuma shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ICPC, Nta Ekpo, da su bayyana gabanta.

Sai dai kuma shugaban hukumar DSS, da ta ICPC ne kawai suka bayyana gaban kwamitin Majalisar wakilan.

A halin da ake ciki, Majalisar ta bawa Ministan Shari’ar nan da ranar Talata ya bayyana gabanta, ko kuma ta dauki mataki a kansa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.