Najeriya

Lauyoyin da ake zargi sun gaza cika sharadodin beli

Mai Shari’a Rita Ofili-Ajugomogbia da ake zargi da Rashawa
Mai Shari’a Rita Ofili-Ajugomogbia da ake zargi da Rashawa

Mai Shari’a Rita Ofili-Ajugomogbia da babban lauyan Najeriya Godwin Obla da ke fuskantar zarge-zarge 30 da suka hada da cin hanci da halarta kudaden haramun, sun kasa cimma sharadodin belin da aka ba su a shari’ar da ake musu yanzu haka a birnin Lagos.

Talla

Mai shari’a Hakeem Oshodi ya bada belin wadanda ake zargin biyu tun ranar 28 ga watan Nuwamba a kan kudi naira miliyan 20 da kuma bada fasfo din su na tafiye tafiye, amma ya zuwa yanzu babu wanda ya iya gabatar da sharadodin.

A zaman kotun yau, lauyan wadanda ake zargi ya nemi a saukaka musu sharadodin belin, matakin da ya sa mai shari’a Oshodi ya mayar da biyan naira miliyan 20 zuwa gabatar da kadarorin da suka kai kudin.

Mai shari’a Rita na daga cikin manyan alkalan kasar guda 7 da hukumar SSS ta yiwa dirar mikiya a gidajen su, inda aka samu makudan kudade da ake zargin na cin hanci ne.

An kuma samu Rita da tura makudan kudade zuwa bankunan kasahsen waje da kuma mallakar wasu kudade da ta kasa bayani akai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.