Najeriya

Mutane 200 sun mutu a ruftawar wani Coci a Najeriya

Ginin cocin da ya rufta da jama'a a birnin Uyo da ke Akwa Ibom ta Najeriya
Ginin cocin da ya rufta da jama'a a birnin Uyo da ke Akwa Ibom ta Najeriya premiumtimesng.com

A Najeriya yawan wadanda suka rasa rayukansu a garin Uyo da ke kudancin kasar, sakamakon ruftawar wata Mujami’a ya karu, daga 50 zuwa 200.

Talla

Daruruwan mutane ke cikin Mujami’ar, ciki harda gwaman jihar ta Akwa’ibom, Udom Emmanuel, da aka gayyata a matsayin babban bako wajen bikin nadin limamin cocin a matsayin Bishop da ya tsallake rijiya da baya, da rauni a ka, biyo bayan rubzawar cocin da ba’a kammala gininsa ba.

Gwamna Emmanuel ya ce dole a gudanar da bincike domin gano ko an aikata almundahana yayin gudanar da ayyukan ginin.

 

Jami’an bayar da agajin gaggawa na ci gaba da aikin ceto don zakulo wadanda buraguzai suka danne.

Tuni aka garzaya da wadanda lamarin ya ritsa da su zuwa asibiti, in da kuma aka ajiye wasu a dakin ajiye gawarwaki da ke birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.