Najeriya

Ministan tsaron Najeriya ya musanta umurnin yiwa hafsoshin sojin kasar ritaya

Ministan tsaron Najeriya Birgediya Mannir Muhammad Dan-Ali mai ritaya
Ministan tsaron Najeriya Birgediya Mannir Muhammad Dan-Ali mai ritaya

Ministan tsaro na tarayyar Najeriya, Birgediya Janar Mansur Muhammad Dan-Ali mai ritaya, ya karyata jita-jitar da ke yaduwa a kafafen sadarwar zamani, da ke cewa ofishinsa, ya aike da tarkadu zuwa wasu manyan hafsoshin sojin kasar, bisa umurnin sauka daga mukaminsu, da shirin yin ritaya.

Talla

Labaran da ke zagaye a wasu kafafen sadarwar zamanin na cewa, Ministan tsaron na Najeriya, ya aikewa da babban hafsan tsaron sojin kasar, Janar Abayomi Gabriel Olanisakin da kuma babban hafsan sojin ruwa Ibok-ete Ekwe Ibas tarkadun basu umarnin mika ofisoshinsu a ranar, ko kuma kafin 16 ga watan Disamba.

Kakkakin ma’aikatar tsaron Najeriya Kanal Tukur Gusau ya ce babu wata magana makamanciyar wadda ake yadawa tsakanin ma’aikatar da ofisoshin hafsoshin sojin, dan haka labari ne kawai marar tushe.

Sanarwar ta ma’aikatar tsaron ta fitar ta ce, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne kawai yake da ikon sauya manyan hafsoshin sojin kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.