Najeriya

HRW ta bukaci a saki EL-Zakzaky

Human Right Watch ta bukaci a saki 'yan Shi'a
Human Right Watch ta bukaci a saki 'yan Shi'a AFP PHOTO PIUS UTOMI EKPEI

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta bukaci Najeriya ta kawo karshen dirar mikiyar da ta ke yiwa mabiya Shi’a da kuma bin umurnin kotu wajen sake shugaban ta Ibrahim El Zakzaky.

Talla

Sanarwar kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya ta hukunta wadanda suka aikata laifi wajen afkawa 'yan Shi’ar da kuma aiwatar da umurnin kotu na sakin shugaban kungiyar da matar sa.

Kungiyar ta ce ta sa baki cikin lamarin ne sakamakon rahotan kwamitin binciken da aka kafa wanda ya bayyana cewar sojoji sun yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen afkawa 'yan Shi’ar shekara guda da ta wuce.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.