Najeriya

Kungiyar SERAP ta yi korafi bisa rashin tantance Ibrahim Magu

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu
Mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

Wata kukngiyar fafutukar tabbatar da adalci da ke amsa sunan SERAP, ta rubuta takardar korafi zuwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kare hakkin dan’adam, bisa abinda ta ce rashin adalcin da Majalisar dattawan Najeriya ke yiwa mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Talla

Kungiyar ta SERAP, ta ce kin amincewar da zauren majalisar dattawan yayi, na tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yiwa yaki da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, manufa ce kawai ta siyasa amma ba bisa cancantar yin hakan ba.

Cikin takardar Korafin da Babban daraktan Kungiyar, Adetokunbo Mumini ya sanyawa hannu, ya ce matakin Majalisar dattawan Najeriyar na kin saurarar Magu domin kare kansa bisa zarge zargen da ake masa, ya tauye ‘yancin da yake da shi kamar na kowane dan kasa.

Majalisar dattawan Najeriya ta dage tabbatar da Ibrahim Magu bisa mukamin shugaban EFCC, bayan rahoton da ta ce ta samu, wanda ke bayyana wasu zarge zarge kansa, ciki harda kama gidan da ya ke zaune a ciki a kan kudi naira miliyan 40 yayinda ake biyan naira miliyan 20 a matsayin kudin hayar gidan duk shekara, wanda kuma rahoton ya kara da cewa wani da ake zargin mai laifi ne ke biyan kudin hayar.

To sai dai kuma kungiyar SERAP ta ce, binciken da ta gudanar ya nuna cewa, Ma'aikatar raya babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja, ke biyan kudaden hayar gidan da Ibrahim Magu ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI