Bakonmu a Yau

Dr. Abdullahi kan shirin bada Naira dubu biyar a Najeriya

Sauti 03:32
Tsabar kudin Naira na Najeriya.
Tsabar kudin Naira na Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya ta fara biyan Naira dubu biyar ga ‘yan kasar da ba su da galihu domin cika alkawuran da ta dauka na rage radadin talauci tsakanin al'umma. Karkashin shirin dai gwamnatin za ta dauki nauyin biyan mutane miliyan guda ne, to sai dai ta fara shirin ne da jihohi guda tara. A game da muhimmancin wannan shirin ne da kuma daurewarsa, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr. Isa Abdullahi na sashin nazarin tattalin arziki da ke jami’ar Kashere a jihar Gombe ta Najeriya.