Bakonmu a Yau

Barr. Muhammad Mudi Mailumo

Sauti 03:46

Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta kafa wani kwamitin mai mambobi 23 domin samar da shawarwari kan yadda za a kare martabar wannan sana’a ta lauya, lura da yadda ake samun kauce wa ka’ida a cikinta.

Talla

Sau da dama dai kungiyar na bayyana damuwa a game da halayen da wasu lauyoyi ke nunawa da kuma kin mutunta dokokin da ke tafiyar da wannan aiki.

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin reshan jiha, Barrister Muhammad Mudi Mailumo, ya ce tabbas akwai gyare-gyaren da ya kamata a yi a wannan aiki a zantawarsa da Abdulkarim Shikkal.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.