Najeriya-Taiwan

Najeriya ta yanke alakar Diflomasiya da Taiwan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP PHOTO / STRINGER

Gwamnatin Najeriya ta yanke alakar Diflomasiya tsakaninta da Taiwan domin nuna goyon bayanta ga kasar China da ke kallon tsibirin na Taiwan a matsayin yankin kasarta.

Talla

Tuni kuma Ministan harkokin wajen Najeriya Goeffry Onyeama ya bukaci mayar da ofishin Taiwan zuwa Birnin Legas daga garin Abuja.

Sai dai kuma Taiwan ta soki matakin da Najeriya ta dauka na yanke huldar Diflomasiyar da ita da kuma shirin rufe ofishin jakadancinta da ke Abuja.

A cewar Taiwan wannan wani yunkuri ne da kasar China ke yi wajen gani ta dangula alakarta da fitar da ita da karfi daga kasashen Nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI