Najeriya-Boko Haram

Shekau ya dau alhakin harin jami’ar Maiduguri

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Abubakar Shekau ya dau alhakin harin jami'ar Maiduguri
Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Abubakar Shekau ya dau alhakin harin jami'ar Maiduguri REUTERS/IntelCenter/Handout

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ce, su suka kai harin kunar bakin wake da ya yi sanadi ran wani Ferfessa da wasu mutane Uku a Jami’ar Maiduguri.

Talla

Shekau ya ce sun kai hare ne saboda aikata ayyukan kafirci a cikin masallaci kuma ba za su dai na kai hari kan duk wanda ke hada Musulunci da kafirci ba.

Sakon murya na tsawon minti kusan 20 da Shekau ya fitar ya ce sun kai hari saboda "ana yin dimokuradiyya a cikin masallacin, mu kuma muna adawa da dimokuradiyya".

Abubakar Shekau ya kuma musanta cewa an kashe mayakan su a dajin Sambisa,  yana mai cewa ''ina rayuwar daram a cikin garin Maiduguri cikin koshin lafiya''.

Shekau ya ce ba ya tsoron gwamnati, kuma ba zai karaya ba har sai ya ga ya rusa tsarin dimokuradiyya a Najeriya.

Harin ranar litinni da ta gabata a masallacin jami’ar Maiduguri ya jikkata mutane 17 bayan wadanda suka kwanta dama.

Wanann ba shine karon farko da Boko Haram ke irin wannan ikirarin a fai-fai bidiyo ko sakon muryar da suke wallafawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.