Najeriya

Sojoji sun ceto dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a Ogun

Babban hafsan Sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai
Babban hafsan Sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai AFP PHOTO/STRINGER

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da ceto dalibai da malaman makarantar Nigeria-Turkish school 8 da akayi garkuwa da su a Jihar Ogun.

Talla

Kakakin rundunar ‘Yan Sandan da ke Jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya bayyana wannan nasarar da rundunar ta samu na ceto daliban da malaman su da ran su.

Jami’in ya ce nan gaba za suyi cikaken bayani dangane da lamarin da kuma halin da daliban ke ciki.

An dai sace wadannan daliban ne a ranar 13 ga watan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.