Najeriya

An kai harin bam a Masallacin Maiduguri

Ana zargin Boko Haram da ci gaba da kaddamar da hare-hare a birnin Maiduguri
Ana zargin Boko Haram da ci gaba da kaddamar da hare-hare a birnin Maiduguri STRINGER / AFP

Wani maharin kunar bakin wake ya kai farmakin bam a wani Masallaci da ke unguwar Dalori Kwatas da ke birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya mai  fama da rikicin Boko Haram.

Talla

Harin wanda aka kai a dai dai lokacin sallar asuba, ya yi sanadiyar mutuwar dan kato da gora guda, bayan ya hana maharin shiga cikin Masallacin.

Wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya shaida mana cewa, maharin ya rungumi dan kato da goran ne da ke gadin masallata, in da bam din ya tashi da su biyun kuma maharin ya yi kaca-kaca.

Tuni dai jami’an hukumar bada agajin gaggawa na kasar suka isa in da lamarin ya faru.

Ana zargin mayakan Bokon Haram da ci gaba da kai farmaki a wurare daban daban na jihar Borno, abin da ke haddasa asarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.