Najeriya-Africa ta Kudu

Daliban Najeriya sun bukaci ficewar kamfanonin Africa ta Kudu

Hari kan baki a kasar Africa ta kudu
Hari kan baki a kasar Africa ta kudu ibtimes.co.uk

Kungiyar Dalibai a Najeriya ta bai wa kamfanonin kasar Africa ta Kudu da ke Najeriya kwanaki biyu su tattara kayansu don barin kasar.

Talla

Daliban sun sanar da hakan ne, yayin zanga-zangar da suka gudanar a harabar ofishin kamfanin sadarwa na MTN mallakin kasar da ke birnin Abuja a yammancin jiya Alhamis.

Gangamin ya biyo bayan rikicin da ke gudana a Africa ta Kudu inda aka tabbatar da kashe wasu ‘yan Najeriya tare da fasa shagunansu hadi wawashe musu dukiya.

To sai dai a tsokacin da ya yi yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, wani masanin siyasa a Najeriya Comrade Isah Tijjani, ya ce “idan bera da sata to daddawa ma da wari”, kamar yadda masu iya Magana ke cewa.

A cewar Comrade Tijjani, halayyar rashin kyawun dabi’a da aikata masha’a a kasar da wasu ‘yan Najeriya ke yi a kasar Africa ta Kudun abin dubawa ne, kasancewar shi ganau ne kan yadda wasu ‘yan Najeriyar ke aikata masha’a ta yadda dole hankalin mai tunani ya tashi.

Dan haka ne ya bukaci ofhin jakandancin Najeriya ya dauki matakin kawo karshen wannan matsala domin samun kwanciyar hankalin ‘yan kasar a Africa ta Kudun.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.