An mallakawa gwamnati motocin Dikko Inde
Wata kotu dake Kaduna a Najeriya ta bada umarnin wucin gadi na mallake motocin kasaita 17 da aka gano a gidan tsohon shugaban hukumar kwastam Abdullahi Dikko Inde.
Wallafawa ranar:
Mai shari'a SM Shuaibu na Babbar kotun tarayya dake Kaduna ya bada umurnin kamar yadda Hukumar EFCC ta bukata.
Alkalin ya ce an mallakawa gwamnatin Najeriya wadannan motoci 17 wadanda za'ayi amfani da su a matsayin shaida a tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban kwastam na halarta kudaden haramun.
A wannan makon ne Hukumar da ke Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC ta sanar da kwace motoci 17 na kasaita daga hannun tsohon shugaban hukumar kwastam.
Mai Magana da yawun hukumar Wilson Uwujeran yace an gano motocin ne a wani gida da Dikko ya mallaka dake Kaduna sakamakon bayanan da suka samu cewar an boye kudi da dukiyar sata a ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu