An rantsar da Amina Muhammed
Wallafawa ranar:
An rantsar da tsohuwar ministan muhallin Najeriya Amina Muhammed a matsayin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.
Sakatare Janar Antonio Guterres ya rantsar da ita, bayan nadin da ya mata a watan jiya.
Amina Muhammed ita ce mace ta biyu da za ta rike wannan mukamin bayan Asha-Rose Migiro ‘yar kasar Tanzania da ta rike mukamin a karkashin Ban Ki Moon tsakanin 2007 zuwa 2012., ta kuma maye gurbin Jan Eliasson na kasar Sweden karkashin shugabancin Ban Ki-Moon.
Ana ganin Amina za ta taka muhinmiyyar rawa na kawo sauyi da zai kunshi daidaito musanman ‘yancin mata.
Amina Muhammed ta rike mukamin ministar Muhalli a Najeriya kafin zama mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu