Najeriya

An sami baraka tsakanin magoya bayan shugabanin Najeriya

An sami baraka tsakanin magoya bayan shugabanin Najeriya.
An sami baraka tsakanin magoya bayan shugabanin Najeriya. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI

Yanzu haka takaddama ta kaure a Najeriya tsakanin magoya bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari da magoya bayan Mukaddashin shugaban Yemi Osibanjo, kan rikon kwaryar da aka bashi sakamakon rashin lafiyar Buhari.

Talla

Yayin da wasu ke yabawa mukaddashin shugaban kasar Osibanjo kan matakan da ya ke dauka cikin kankanin lokaci, wasu na cewa ai duk wani mataki da ya ke dauka, umurni ne daga mai gidan sa Buhari.

Wannan ya sa mai taimakawa shugaban kasar Babafemi Ojudu ya ce duk wani mataki da Osibanjo ke dauka sai ya tuntubi Buhari kafin ya aikata.

Duk wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Buhari ke ci gaba da jinya a Birnin Landan na Britaniya da ya kwashi kusan wata daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI