Najeriya

Onnoghen ya kafa tarihi bayan zama Alkalin alkalan Najeriya

Sabon Alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Walter Onnoghen
Sabon Alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Walter Onnoghen guardian.ng

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Mai shari'a Walter Onnoghen a matsayin sabon Alkalin alkalan Najeriya.

Talla

Hakan ya bai wa mai shari’a Onnoghen dan jihar Cross River, damar zama mutum na farko daga kudancin Najeriya da ya samu wannan matsayi cikin shaker 30 da suka gabata.

Alkalin alkalan Najeriya na karshe daga kudancin Najeriya, mai shari’a Ayo Irikefe, ya rike matsayin ne a shekara ta 1987.

A ranar 7 ga watan Fabarairun da ya gabata, mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya rubutawa majalisar dattawan kasar wasika, bisa bukatar a tabbatar da mai shari’a Onnoghen a matsayin Alkalin alkalan kasar.

Tun da fari, a ranar 13 ga watan Oktoban shekara ta 2016, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da karawa Onnoghen matsayin Alkali mafi daraja a kotun kolin Najeriya, daga bisani kuma ya zama mukaddashin Alkalin alkalan Najeriya a ranar 10 ga watan Nuwamba da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI