Bakonmu a Yau

Shugaban Miyetti Allah reshen Borno Musa Maina Harande

Sauti 03:34
An sace Shanun Fulani sama da dubu goma a rikicin Boko Haram
An sace Shanun Fulani sama da dubu goma a rikicin Boko Haram RFI Hausa/Awwal

Wasu alkalumma da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen Jihar Borno ta tattara sun bayyana cewa kimanin Shanu sama da dubu goma ne mayakan Boko Haram suka sace a sassan jihar da kuma awaki da tumaki kusan dubu Talatin. A baya dai, ‘yan Boko Haram sun koma satar Shanu domin samun abincin da zasu ci, matakin da ya sa gwamnatin Borno ta rufe kasuwar Shanu a sassan Jihar. Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Borno Musa Maina Harande ya shaidawa Awwal Janyau yawan hasarar shanun da Fulani suka yi a rikicin Boko Haram.