Najeriya-Africa ta Kudu

Tsagerun Niger Delta sun yi barazanar daukar fansa kan Africa ta Kudu

Daya daga cikin tsagerun yankin Niger Delta a kudancin Najeriya
Daya daga cikin tsagerun yankin Niger Delta a kudancin Najeriya Reuters/Flora Shaw

Wasu kungiyoyin tsagerun yankin Niger Delta a Najeriya, sun yi barazanar, amfani da bam wajen tarwatsa wasu kamfanonin Africa ta Kudu a matsayin martani kan barnar da akai wa ‘yan Najeriya a kasar.

Talla

Tsagerun Niger Delta dai sun baiwa hukumomin Najeriya wa’adin wata guda su rufe kamfanonin kasar Africa ta Kudun ko kuma su lalata su.

Wannan na zuwa a dai dai lokacin da majalisun Najeriya suka kafa tawagar da zata gana da hukumomin Africa ta Kudu kan wannan matsala.

Sai dai yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa na sashin nazarin kumiyyar siyasa da ke jami’ar Bayero a Najeriya, ya ce za’a tafka babban kuskure muddin aka ce za’a maida martani bata hanyar lumana ba, kan harin da wasu yan Africa ta Kudu suka kaiwa ‘yan Najeriya.

A cewar Dr Dukawa wajibi ne awarware matsalar ta hanyar diflomasiya, wajen gudanar da sahihin binciken musabbabin matsalar, a kuma tantance zargin da ‘yan Africa ta Kudun ke wa ‘yan Najeriya bisa bata musu kasa, da ya kunshi tu’ammuli da kwayoyi da masha’a.

Dr Dukawa ya ce ta hanyar Diflomasiyya ne kawai za’a tabbatar daukar matakan adalci ga dukkanin bangarorin da matsalar ta shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.