Najeriya

Kamfanonin mai za su tare a Niger Delta na Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bukaci kamfanonin man fetir na kasashen waje da su koma da shalkwatarsu zuwa Niger Delta
Gwamnatin Najeriya ta bukaci kamfanonin man fetir na kasashen waje da su koma da shalkwatarsu zuwa Niger Delta AFP/ Pius Utomi Ekpei

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bai wa kamfanonin man fetir na kasashen waje da ke aiki a kasar da su mayar da shalkwatarsu zuwa Niger Delta don rage rikicin da ake fama da shi a yankin.

Talla

Osinbajo ya bada umarnin ne a yayin wani taro da ya halarta a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ziyarar da ya ke ci gaba da ya yi a yankin don ganawa da masu ruwa da tsaki.

Mukaddashin shugaban ya bukaci karamin ministan mai na kasar Dr.Ibe Kachikwu da ya fara kaddamnar da shirin sauya wa kamfanonin matsuguni a Niger Delta.

Osinbajo ya ce, “Ina zaton wannan makin ya yi dai dai”.

A game da shirin gwamnatin kasar kan yi wa tsoffin mayakan Niger Delta afuwa kuwa, Farfesa Osinbajo ya jaddada cewa, ma’aikatar man fetir ta kasar da ofishin kula da shirin afuwar na aiki tare da gwamnatocin Niger Delta don ganin matasa sun ci gajiyar shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI