'Yan kunar bakin wake sun mutu a Maiduguri
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wasu wata uku maharan kunar bakin wake sun rasa rayukanu bayan daya daga cikinsu ta tada bam din da ke jikinta a kusa da wasu tankokin mai a safiyar yau a birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Tankokin man guda biyu da aka ajiye su akan hanyar Damboa sun kone kurmus sakamakon aukuwar lamarin.
Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Abdulkadir Ibrahim, ya ce, tuni aka kwashe gawarwakin maharan na kunar bakin wake.
Ibrahim ya ce, an kuma shawo kan gobarar da tashin bam din ya haddasa, yayin da wasu majiyoyi ke cewa, harin bai shafi jama'a ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu