Najeriya

Kotun Majistare a Najeriya ta sallami masu fafutukan kafuwar Biafra 35

Hoton marigayi madugun 'yan tawayen Biafra Kanar  Odumegwu Emeka Ojukwua lokacin da yake jawabin ballewa daga Najeriya
Hoton marigayi madugun 'yan tawayen Biafra Kanar Odumegwu Emeka Ojukwua lokacin da yake jawabin ballewa daga Najeriya AFP Archives

A Nigeria wata kotun Majistare dake Fatakwal ta sallai wasu mutane 35 dake tsare saboda fafutukan neman kasar  Biafra  daga Najeriya.

Talla

Kamfanin Dillancin labaran Nigeria, NAN na cewa mutanen na tsare ne tun ranar 20 ga watan Janairu na wannan shekara a lokacin da suke zanga-zangan nuna farin cikinsu da nasarar zaben Donald Trump na Amurka wanda suke ganin zai taimaka a sami kasar Biafra daga Najeriya.

Alkalin Kotun Andrew Jaja a lokacin da yake sallaman mutanen ya ce sun kwashe kwanaki 37 a tsare ba tareda wasu kwararan hujjoji ba daga masu bincike.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI