Najeriya

Daruruwan 'yan gudun hijira sun yi zanga zanga a Borno

Daruruwan ‘yan gudun hijirar Boko Haram mafi yawansu mata ne suka gudanar da zanga zangar neman a kyautata rayuwarsu a cikin sansanonin da ke Maiduguri a jihar Borno.

Wasu 'yan gudun hijirar Boko Haram a Borno, Najeriya.
Wasu 'yan gudun hijirar Boko Haram a Borno, Najeriya. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

'Yan gudun hijirar sun gudanar da zanga zangar ce a daidai lokacin da tawagar Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da ziyarar yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan gudun hijira na sansanin Bakassi da ke Maiduguri, a daidai lokacin da jami’an na Majalisar Dinkin Duniya suka iso ne, masu zanga-zangar suka rika zargin mahukunta da kuma kungiyoyin agaji na gwamnatin Najeriya, da karkata akalar kayayyakin agajin da ake tattarawa da sunansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI