Najeriya

An kaddamar da Dakin Karatu na Miliyoyin kudade na Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo

Mai rikon shugabancin Najeriya  Farfeso Yemi Osibajo ya kaddamar da dakin karatu na miliyoyin kudade da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya kafa harsashin ginawa a garin Abeokuta jihar sa ta usuli.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo AFP / Seyllou
Talla

A watan Nuwamba na shekara ta 2002 Olusegun Obasanjo ya kaddamar da asusun fara ginin dakin karatun kuma bukin budewa ya sami halarcin manyan baki daga ciki da wajen Najeriya.

Shugaban Liberia Uwargida Ellen Johnson Sirleaf a jawabin ta ta ce kaddamar da dakin karatun zai zama abin tarihi ga Najeriya.

Cikin wadanda suka sami halartan bukin kaddamar da dakin karatun akwai tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo, tsohon shugabanin  Benin Boni Yayi, Joyce Banda na Malawi da John Kufor na kasar Ghana.

Akwai kuma tsohon sakatare Janar na MDD Kofi Anan da wasu shugabannin kasashe da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI