Najeriya zata wadata da shinkafa kafin karshen 2018 - Ogbeh
Wallafawa ranar:
Ministan lura da ayyukan noma da raya karkara na Najeriya, Chief Audu Obeh, ya ce kafin isa karshen shekara ta 2018 Najeriya zata dogara da kanta wajen noman shinkafa.
Chief Ogbeh ya bada tabbacin ne, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, a garin Abuja, inda yace hakan na da nasaba da yadda manoma a kasar suka rungumi shirin gwamnati na karfafa noma a kasar.
Ministan ya ce tuni gwamnatin kasar, ta shigo da manyan injinan tsaftace shinkafa sama da dari da goma, kuma nan bada dewaba za’a rarraba su zuwa inda ake bukata a sassan kasar.
Zalika ya ce nan bada dadewa ba manoman kasar, zasu fara samun buhun taki kasa da farashin naira 6,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu