Najeriya

'Yan fashi a kan teku sun saki matuka 'yan kasashen waje da suka kama

Wasu 'yan fashin teku a kasar Somalia
Wasu 'yan fashin teku a kasar Somalia AFP PHOTO / MOHAMED DAHIR

Wasu ‘yan fashi a kan taku a Najeriya, sun saki wasu direbobin jirgin ruwa ‘yan kasar Rasha guda 7 da kuma wani guda dan kasar Ukraine, wadanda suka kama a watan da ya gabata.

Talla

An saki matukan ne bayan tattaunawar tsakanin masu kamfanin jirgin ruwan na daukar kaya da kuma ‘yan fashin a kan teku.

Masana kan harkar tsaro dai sun bayyana yankin tekun yammacin Africa a matsayin daya daga cikin mafi hadari a duniya, inda ‘yan fashi ke hari kan jiragen ruwan da ke safarar mai da kuma sace matuka don karbar kudaden fansa masu yawan gaske.

A shekarar da data gabata dai, kasashen yammacin nahiyar Africa sun sha gudanar da taro kan yadda za'a hada gwiwa wajen magance matsalar fashi a kan taku, da ya haddasawa yankin dimbin hasara musamman wajen satar danyen mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI