Bakonmu a Yau

Daruruwan 'yan gudun hijira sun yi zanga zanga a Borno

Wallafawa ranar:

A daidai lokacin da tawagar Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da ziyarar gani da ido kan halin da rikicin Boko Haram ya jefa mutanen yankin tafkin Chadi, ‘Yan gudun hijira da dama ne mafi yawancinsu mata suka gudanar da zanga-zangar neman kyautata rayuwarsu a cikin sansanoninsu da ke Maiduguri a jihar Borno. ‘Yan gudun hijirar na kukan yadda ake karkatar da kudi da kuma kayayyakin agajin da ya kamata ace sun zo a hannunsu. Wannan na zuwa a yayin da MDD ta kafa gidauniyar kudi dala Biliyan daya da rabi domin tallafawa mutanen tafkin chadi da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu. Awwal Janyau ya tattauna da Grema Terab tsohon shugaban hukumar agajin gaggawa ta SEMA a jihar Borno.  

Manyan motoci makare da kayayyaki da suka hadar da abinci a garejin Muna da ke garin Maiduguri, Nigeria.
Manyan motoci makare da kayayyaki da suka hadar da abinci a garejin Muna da ke garin Maiduguri, Nigeria. REUTERS/Paul Carsten