Najeriya

Najeriya ta shawarci 'yan kasar da su dakata da ziyartar Amurka

Wasu 'yan Amurka da ke zanga zangar nuna adawa da matakin gwamnatin Trump kan hana baki shiga kasar.
Wasu 'yan Amurka da ke zanga zangar nuna adawa da matakin gwamnatin Trump kan hana baki shiga kasar. Spencer Platt/Getty Images/AFP SPENCER PLATT / GETTY IMAGES NORT

Gwamnatin Najeriya ta umurci ‘yan kasar da su kaucewa zuwa kasar Amurka har zuwa wani lokaci nan gaba. 

Talla

Mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yan kasar dake zama a kasashen waje, Abike Dabiri tace umarnin ya zama tilas, ganin yadda aka hana wasu masu rike da bizar shiga kasar tafiya.

Dabiri tace duk wani dan Najeriya dake shirin zuwa Amurka muddin ba bisa ziyarar gaggawa ba, to ya jinkirta tafiya har sai an samu karin haske dangane da sabon shirin karbar bakin kasar.

Najeriya dai bata cikin jerin kasashen da shugaba Donald Trump ya bayyana su a matsayin wadanda aka haramtawa yan kasar zuwa Amurka, sai dai kuma rahotanni sun ce an hana wasu ‘yan kasar shiga.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.