Najeriya

Shirye shiryen fara sufurin jiragen sama daga Kaduna

Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja Najeriya.
Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja Najeriya. guardian.ng

Gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe filin jiragen sama na Abuja a hukumance, tare da sanar da kammala shirin mayar da jigilar fasinjoji zuwa filin jiragen sama da ke jihar Kaduna. Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar gani da ido filin jiragen da ke Kaduna inda ya bayyana gamsuwa da ayyukan inganta filin da aka gudanar.  Sai dai kuma wasu fasinjoji sun bayyana shakku kan cancantar filin jiragen saman na fara karbar jigila daga fannin kasa da kasa. Wakilinmu na jihar Kaduna Aminu Sani Sado ya hada mana wannan rahoton.

Talla

Shirye shiryen fara sufurin jiragen sama daga Kaduna

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI