Najeriya

Andrew Yakubu ya shigar da karar EFCC a kotu

Tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya, Andrew Yakubu
Tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya, Andrew Yakubu

Tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC da ke Najeriya Andrew Yakubu ya gurfanar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC a gaban kotu, in da ya ke bukatar biyan sa diyyar Naira biliyan guda, saboda abin da ya kira cin zarafinsa.

Talla

Yakubu ya gabatar da karar ne a wata babbar kotu da ke Abuja, wadda ta sanya ranar 9 ga watan nan domin sauraron karar.

Lauyan Yakubu, Adeola Adedipe ya ce, suna bukatar kotun ta kuma hana hukumar EFCC ci gaba da gudanar da wani bincike akan sa.

A watan da ya gabata ne hukumar EFCC ta kwace kudaden da suka kai kusan Dala miliyan goma a gidan Yakubu, wanda ake zargi da halarta kudaden haramun.
andrew yakudu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.