Najeriya

Ba mu fatan mutuwar Buhari- PDP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na duba lafiyarsa a birnin London
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na duba lafiyarsa a birnin London AFP PHOTO / SAJJAD HUSSAIN

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce, ba ta son shugaban kasar da ke duba lafiyarsa a birnin London Muhammadu Buhari ya mutu kamar yadda wasu masu ma shi makarkashiya ke fata.

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da shugabannin jam’iyyar ta PDP suka ce, a shirye suke su kai wa shugaba Buhari ziyarar gaisuwa a birnin na London.

A zantawarsa da RFI hausa, shugaban kwamitin amintattu na PDP Sanata Walid Jubril ya ce, ba su yi wa shugaban mugunyar fata, illa a kullum suna gudanar da addu’in fatar ganin Buhari ya dawo don ci gaba da aikinsa na shugaban kasa a Najeriya.

Sanata Walid Jubril kan dawowar Buhari

Jubril ya ce, ba sa adawa da rashin lafiyar da Buhari ke fama da shi, sannan ba sa fatan ya mutu kamar yadda wasu ke yi ma sa don samun madafun iko a kasar.

Julbril ya kara da cewa, su na yi wa Buhari addu’oin samun lafiya a duk wani taro da suka gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.