Bakonmu a Yau

Alhaji Isa Tafida: shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya

Sauti 03:34
michaelweening.com

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani gagarumin shirin farfado da tattalin arzikin kasar da zai samar mata da ci gaba da kuma bunkasa harkokin noma da samar da abinci wanda zai hana ta dogara da kasashen waje. Shirin wanda zai dauki shekaru uku ana aiwatar da shi, tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020, zai taimakawa Gwamnati wajen rage dogaro da man fetur. Ma’aikatar kasafin kudin kasar tace shirin zai kuma taimaka wajen tallafawa masu kananan masana’antu da kananan manoma. Alh Isa Tafida Mafindi, masanin tattalin arziki kuma manomi yayi mana tsokaci akai, yayin zantawarsu da Bashir Ibrahim Idris.